<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu, har ga mutuwa ka kai don cetonmu,
 Ka ƙuje maƙiyinmu kuwa, ka ƃata ikonsa.

[V2]
 2) Ina misalin kayanka? Mai ɗauka, kai kaɗai!
 Ka ɗauke namu zunubai, ta wurin giciyenka.

[V3]
 3) Yanzu ka hau ga Sama can, ka shiga hutawa.
 Allah ya ba ka daraja a hannun damansa.

[V4]
 4) Me za mu kai guri Yesunmu? Mai fansarmu ne shi,
 Baki ya kasa yabonsa, Yesu ne mafifici.

[V5]
 5) Mu miƙa ranmu gaba ɗaya, mu yi ta aikinsa,
 Har ran da zai fyauce mu can a gidan Ubansa.</lyrics>
<title>Ya Yesu, Har Ga Mutuwa Ka Kai Don Cetonmu LW115</title>
<hymn_number>115</hymn_number>
</song>